Jakadan kasar Iran a Mosco ya bayyana cewa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai kawo ziyarar aiki Tehran nan ba da dadewa ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran.
Labarin ya kara da cewa kasashen biyu sun kulla yarjeniyoyi masu yawa a tsakanin daga ciki har da masu dogon zango.
Kazem Jalali ya bayyana a yau Alhamis kan cewa kasar Rashe ce kasa tilo wacce ta zuwa jarin dalar Amurka biliyon $8 a bangaren gas da man fetur. Kuma ya zuwa yanzu ta kashe dala $ 5bl daga cikinsu.
Banda haka zata kashe kudade don kammala layin dogo wacce ake kira hanyar Arewa zuwa Kudu. Banda haka Rasha zata fara tura danyen man fetur daga Rasha zuwa Iran don sayar da shi. Sannan a halin yanzu bankunan kasashen biyu a hadi da na’urori wanda zai bawa mutanen rasha kashe kudadensu a Iran tare da katin Mir a yayinda Iraniyawa zasu kashe kudadensu a Rasha da Katin banki na Shetab.