Shugaban Kasar Iran Ya Yi Suka Kan Siyasar Munafuncin Amurka Da Na Wasu Kasashen Yamma

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Siyasar munafunci ita ce ta sanya yahudawan sahayoniyya suka zama babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Siyasar munafunci ita ce ta sanya yahudawan sahayoniyya suka zama babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban majalisar Tarayyar Turai Charles Michel ya jaddada cewa: Siyasar munafunci na Amurka da wasu kasashen yammacin turai ita ce ta sanya yahudawan sahayoniyya suke da girman kai da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.

Shugaba Masoud Pezeshkian ya jaddada haka ne a yammacin jiya Lahadi yana mai cewa: Makasudin kakabawa kasashe irinsu Iran takunkumai masu tsanani shi ne domin hana zaman lafiya na sabon tsarin duniya.

A nashi bangaren, shugaban majalisar Tarayyar Turai ya bayyana fatansa na fara gudanar da kyakkyawar mu’amala tsakanin Iran da Tarayyar Turai bisa tushen samar da moriyar juna da kawar da cikas ga ci gaba da huldar da ke tsakaninsu, ya kuma jaddada aniyar kasashen Turai na kyautata alaka da dangantakarsu da Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments