Shugaban Kasar Iran Ya Kai Ziyara Zuwa Kasar Oman don Karfafa Kyakkyawar Alakar Kasashen Biyu

Kafin tashinsa zuwa kasar Oman shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna neman kyakkyawar dangantaka da maƙwabtansu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar kafin

Kafin tashinsa zuwa kasar Oman shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna neman kyakkyawar dangantaka da maƙwabtansu

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar kafin ya tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Tehran zuwa birnin Muscat a yammacin yau Talata cewa: Makasudin ziyarar tasa zuwa kasar Oman ita ce kulla kyakkyawar alaka da kasashe makwabta, kuma alaka tsakaninsu tana bunkasa kowace rana.

Shugaba Pezeshkian da yake zantawa da manema labarai a filin tashi da saukar jiragen sama na Mehrabad ya bayyana cewa: A halin yanzu yawan ciniki tsakanin Iran da Oman ya kai dalar Amurka biliyan 2.3, yana mai jaddada bukatar ci gaba da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Pezeshkian ya ce: Zai gudanar da wannan ziyara ce bisa gayyatar da Sultan Haitham bin Tariq Al Said ya yi masa a hukumance, kuma bisa ga dukkanin manufofin gwamnati da Jagoran juyin juya halin Musulunci, manufar wannan ziyara ita ce kulla alaka mai zurfi da kyakykyawan dangantaka da kasashen makwabta ciki har da masarautar Oman, haka kuma an shirya fadada dangantakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a dukkanin bangarori na siyasa da tattalin arziki da zamantakewa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments