Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Burunsu Na Samar Da Hadin Kai Tsakanin Al’ummun Kasashe

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Babban burinsu shine samun haɗin kai da dunkulewa waje guda da kuma samun aminci a tsakanin                        al’umma Shugaban kasar

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Babban burinsu shine samun haɗin kai da dunkulewa waje guda da kuma samun aminci a tsakanin                        al’umma

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Manufofin da suka Sanya a gaba domin cimma su a yayin ziyarar da suka kai zuwa makwabciyarsu kasar Iraki cikin kwanakin da suka gabata, su ne samar da hangen nesa guda, hadin kai da taimakekkeniya.

A rubutun da ya yi da harsunan Larabci da kurdanci a shafinsa na dandalin “X” Shugaban na Iran ya bayyana cewa: A yayin wannan ziyara an sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa guda 14 tsakanin Iran da Iraki.

Ya kara da cewa: Babban burin Iran na gaggawa shi ne samar da harshe guda da hangen nesa kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu. Akwai tarurruka masu kyau a Iraki da ke haifar da karin hadin kai da karfin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa: Babban burin Iran shi ne samun hadin kan al’umma da hadin gwiwa da kuma fahimtar juna a tsakanin al’ummar musulmi baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments