Shugaban Kasar Iran Ya Ce Akwai Bukatar Kara Yawan Haihuwa A Kasar Saboda Tsaro Da Kuma Nasara Kasar

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana muhimmancin aure da haihuwar matasa a kasar, don haka yana da muhimmanci ga tsaro da kuma samun

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana muhimmancin aure da haihuwar matasa a kasar, don haka yana da muhimmanci ga tsaro da kuma samun nasara a shirye shiryen gwamnati, matasa su yi aure su kuma haihu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a wani taron matana a nan birnin Tehran. Ya kuma kara da cewa gwamnati tana da shirye shirye na musamman don ganin matasa sun yi aure sun kuma haifu, da kuma tallafi na musamman ga wadanda suke son Karin haihuwa don yawaita mutanen kasar.

Shugaban ya bayyana rashin amincewarsa da zabar da ciki, ya kuma kara da cewa yawan mutanen ko wace kasa a duniya na da dangantaka da irin nasaran da kasar zata sami kan makiyanta, da kuma ci gaban kasar.  Yace addinin musulunci yana bada matukar mihimmanci ga samar da iyala da kuma tallafa masa don daga nan ake gina al-umma.

Daga karshen shugaban ya kammala da cewa ‘ shi’arin wannan shekara ta 1403’ ita ce” yawaita samar da kayaki daga cikin kasa tare da taimakon mutanen kasar’. Wanda yake nuna irin rawan da mutane suke takawa a ci gaba da tsaron ko wace kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments