Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Turkiyya ReJab Tayyip Erdogan kan mutanen da suka mutu a gobarar da ta yi sanadin mutuwar wasu ‘yan kasar Turkiyya.
A cikin wannan sakon ta hanyar wayar tarho, shugaba Pezeshkian ya bayyana cewa, ya shiga cikin gagarumin alhini da kuma bakin ciki da samun labarin aukuwar gobarar da ta afku a wani otel da ke birnin Bolu, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama ciki har da matafiya, yana mai mika ta’aziyyarsa ga takwaransa na Turkiyya da iyalan wadanda abin ya shafa, da daukacin al’ummar Turkiyya abokai ‘yan uwan junan al’ummar Iran.
Shugaba Pezeshkian ya yi addu’ar samun rahama da gafara ga wadanda abin ya shafa, da hakuri da kuma jaje ga iyalansu, gami da fatan samun sauki cikin gaggauta ga wadanda suka jikkata. Ministan cikin gidan Turkiyya ya sanar da cewa adadin wadanda gobarar ta shafa ya kai mutane 76.