Shugaban kasar Iran Raisi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Shugaban Rasha Putin

A lokacin zantawar ta su shugaban kasar iran Ibrahim Ra’isi ya jinjina game da muhimmacin alakar dake tsakanin kasashen Rasha da iran musamman idan aka

A lokacin zantawar ta su shugaban kasar iran Ibrahim Ra’isi ya jinjina game da muhimmacin alakar dake tsakanin kasashen Rasha da iran musamman idan aka yi la’akari da irin yadda suka yi tarayyar  a wasu kungiyoyi na kasa da kasa kamar kungiyar kadin kai na kasashen Shanghai da kuma Biricks ,don haka jadda game da muhimmancin aiki da yarjoniyoyin da aka kulla tsakaninsu  da suka hada da shinfada layin dogo na Rasht Astara.

Haka zalika Raisi ya taya shugaba putin murnar sake lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar kana ya bayyana fatansa na ganin sabuwar gwamnatin rasha za ta saka share sabon fage na fadada danganata dkae tsakaninsu  da kuma yin aiki tare tsakanin kasahen biyu a bangarorin daban daban.

Ana sa bangaren shima shugaban rasha ya tayi takwaransa na iran murnar fara Azumin watan Ramadan  da kuma sabuwar shekarar iraniyawa ta shamasiyya, yace an kusa kammala daftarin cikakkayar yarjejeniy hadin guiwa tsakanin iran da rasha , kana ya bayyana nasarar da aka samu a taron hadin guiwa kan tattalin arziki da aka yi a birnin Tehran , da kuma karuwar cinikiyyar kayayyaki da kashi77 cikin 100 tsakanin kasahen biyu a matsayin alamu na samun ci gaba mai kyau tsakanin kasashen biyu

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments