Shugaban Kasar Iraki Ya Bayyana Cewa Shahadar Shugaba Ra’isi Musiba Ce Ga Dukkan Kasashen Yankin

Abdullatif  Rasheed shugaban kasar Iraki wanda yake ziyarar ta’aziyyar rasuwar shugaba Ibrahim Ra’isi a nan Tehran ya bayyana cewa rasuwar shugaba Ra’isi musiba ce ga

Abdullatif  Rasheed shugaban kasar Iraki wanda yake ziyarar ta’aziyyar rasuwar shugaba Ibrahim Ra’isi a nan Tehran ya bayyana cewa rasuwar shugaba Ra’isi musiba ce ga kasashen yankin gaba daya.

Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya nakalto shugaba Rasheed ya na fadar haka a lokacinda yake ganawa da shugaban rikon kwarya na kasar Iran Muhammad Mukhbir a ofishiunsa a jiya Asabar a nan birnin Tehran.

Rasheed ya kara da cewa rasuwar shugaba Ra’isi musiba ce ga mutanen Iran a matakin farko, amma mutanen kasar Iraki da sauran kasashen yankin duk sun kadu da shahadar shugaban.

Daga karshe ya Rasheed ya jadda cewa gwamnatin kasar Iraki zata ci gaba da aiwatar da dukkan yarjeniyoyin da aka cimma da kasar Iran a zamanin shugaba Ra’isi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments