Shugaban Iran Ya Gargadi ‘Yan Sahayoniyya Kan Gigin Kai Hari Kan Kasarsa

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Duk wani kuskuren da ‘yan  sahayoniyya zasu aikata zai fuskanci mayar da martani mai tsauri daga Iran Shugaban kasar

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Duk wani kuskuren da ‘yan  sahayoniyya zasu aikata zai fuskanci mayar da martani mai tsauri daga Iran

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Ci gaba da aikata laifukan da yahudawan sahayoniyya suke yi, zai kara fuskantar mayar da martani mai zafi daga sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai fayyace cewa; Idan har wannan ja’irar gwamnati ta kara aikata wani dan karamin kuskure, to za ta fuskanci mafi tsanani da karfi martani.

Wannan gargadi na shugaban kasar ta Iran ya zo ne a yayin jawabinsa a yammacin jiya Laraba da wata babbar tawaga ta ‘yan kungiyar gwagwagrmayar Musulunci ta Hamas a birnin Doha na kasar Qatar.

Pezeshkian ya kara da cewa: Shahadar Isma’il Haniyeh shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas na daya daga cikin abubuwan da suka yi zafi a rayuwarsa, yana cewa: Sanar da shi kisan gillar da aka yi Isma’il Haniyya ya kona masa zuciya.

Yana mai jaddada cewa: Laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suka aikata a baya-bayan nan a Gaza da Lebanon ta hanyar zubar da jinin bil’Adama abin firgici ne da suka kona zukata, yana mai bayanin cewa: Wannan zafi ya ninka a zukatansu domin al’umma suna da tabbacin cewa An zalunci al’ummar baya ga yadda Iran take daukansu a matsayin ‘yan uwa na addini.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments