Shugaban Iran Ya Ce: Karfin Kasarsa Ne Ya Sa Ake Shayin Daukan Matakin Wuce Gona Da Iri Kanta

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin da Iran ke da shi na karfin mayar da martani ya karya karfin gwiwar makiyanta wajen tunkararta A

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin da Iran ke da shi na karfin mayar da martani ya karya karfin gwiwar makiyanta wajen tunkararta

A safiyar yau Asabar ne aka fara gudanar da faretin sojojin kasar Iran a gaban shugaban Jamhuriyar musulinci ta Iran, Masoud Pezeshkian, wanda aka fara gudanar da makon tsaro mai alfarma da kuma murnar zagayowar ranar haihuwar manzon Allah (s.a.w) a haramin wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci Imam Khumaini (Yardan Allah ya tabata a gare shi).

A yayin bikin faretin sojojin na kasar Iran, wanda aka gudanar a safiyar yau Asabar a daidai lokacin da aka fara gudanar da makon tsaro mai alfarma (ranar tunawa da mayar da martani ga kazamin yakin da gwamnatin Saddam ta kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a lokacin wato shekara ta 1980 zuwa shekarar1988), a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke birnin Rey a shiyar kudancin birnin Tehran fadar mulkin kasar, shugaban kasar Masoud Pezeshkian ya yi addu’a ga marigayi Imam (Allah ya kara masa yarda) shi) da ruhin sauran shahidai, tare da taya jagoran juyin juya halin Musulunci mai hangen nesa da al’ummar Iran, murnar fara makon tsaro mai alfarma.

An fara bikin ne da karatun ayoyin kur’ani mai tsarki, wanda ya samu halartar manyan kwamandojin sojoji, hafsoshin soji na wasu kasashe da                                   suka zo Iran, da tawagar iyalan shahidai, da wadanda suka samu raunuka a wajen yaki, da kuma tsoffin sojoji.

A cikin jawabinsa a wajen bikin, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Karfin ikon Iran da kariya ne ya sanya ba zai yiwu wani shaidani ya kaddamar da yaki kan kasar Iran mai daraja ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments