Shugaban Iran Ya Aike Da Wasika Ta Musamman Zuwa Ga Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya

Hukumar kula da aikin hajji ta kasar Iran ta bayyana cewa shugaban ga yarima mai jiran gado na kasar Saudiya  Mohammad Bin Salman a wata

Hukumar kula da aikin hajji ta kasar Iran ta bayyana cewa shugaban ga yarima mai jiran gado na kasar Saudiya  Mohammad Bin Salman a wata ziyara da suka kai birnin Riyadh a baya bayan nan.

Wannan sakon yana nuna irin kokarin da ake yi ne na ganin an daidaita da kuma  kara yin aiki tare tsakanin Riyadh da Tehran, bisa la’akari da irin tattaunawa da aka yi a shekarar bara, diplomasiya ta addinin dake kewaye da aikin hajji na shekara –shekara ta kasance mai muhimmanci don samar da zaman lafiya .

Ali reza Rashidiyan shugaban hukumar aikin hajji ta kasar iran ya kai ziyara kasar saudiya ne domin rattaba hannu kan shirye- shiryen jerjejeniyar aikin hajji da zaa yi a shekara ta 2026, kuma ya jaddada cewa zai ci gaba da bin tsarin da aka yi amfani da shi a shekara da ta gabata ,yayin da jami’an saudiya suka yi alkawarin bada cikakken hadin kai da ake bukata.

Yarjejeniyar da aka kulla ta kunshi gidaje, sufuri, da kuma kayayyakin abinci , kiwon lafiya da sauran abubuwan dake bukata a birnin mai tsarki, babban burin iran shi ne kammala dukka  shirye shirye a watan sha’aban kuma yayi alkwarin yin aiki tukuri a lokacin aikin hajji,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments