Shugaban Colombia Gustavo Petro ya yi kira da a kafa rundinar soji ta kasa da kasa don ‘yantar da Falasdinu da adawa da ‘yan mulkin kama karya da Amurka da NATO ke yadawa.
A jawabin da ya gabatar a zauren MDD, Petro ya bukaci kasashen da ke adawa da kisan kiyashi da su hada karfi da karfe, domin kare rayukan al’ummar Palasdinu.
“Muna bukatar sojoji masu karfi da suka kunshi kasashen da ba su amince da kisan kare dangi ba, Dole ne mu ‘yantar da Falasdinu,” in ji shi.
Petro ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda ayyukan Washington da NATO ke gurgunta mulkin dimokuradiyya da kuma taimakawa wajen sake dawo da mulkin kama-karya a duniya.
Kiran da Petro na hada kawancen soji ya yi daidai da irin wannan shawarar da shugaban kasar Indonesiya Prabowo Subianto ya bayar, wanda ya bayyana aniyarsa ta samar da dakaru 20,000 da za ta iya girkewa a Gaza.
A ranar Talata shugaban kasar Chile Gabriel Boric ya bayyana muradinsa na ganin an gurfanar da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a gaban kotun kasa da kasa kan kisan kiyashi a zirin Gaza kan kisan kiyashi a Gaza.