Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Akwai yiwuwar nan gaba kasar Ukraine ta iya zama wani bangare na tsarin tsaron kasar Rasha
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a ranar Litinin cewa: Dole ne kasar Ukraine ta tabbatar da tsaron kudaden Amurka da aka zuba a cikinta, saboda zata iya zama karkashin kasar Rasha wata rana.
Trump ya kara da cewa a yayin zantawarsa da Tashar talabijin ta Fox News; Suna da kasa mai kimar gaske mai dauke da ma’adanai na musamman da man fetur da kuma iskar gas, da sauran abubuwa.
Trump ya ci gaba da cewa: Yana son dukiyarsu ta kasance cikin aminci, domin suna kashe daruruwan biliyoyin dalolia cikin kasar.
Ya karkare furucinsa da cewa; Za su iya cimma yarjejeniya, watakila ba za su iya ba. Wata rana za su iya zama wani ɓangare na kasar Rasha, akwai kuma yiwuwar hakan ba zai kasance ba.