Shugaba Kasar Lebanon Ya Ce Kungiyar Hizbullah Bata Da Zabi Sai Abinda Gwamnati Ta fada

Shugaban kasar Lebanon Josept Aoun ya bayyana cewa gwamnatinsa tana son ta maida makamai a kasar Lebanon karkashin ikon hukuma kadai. Aoun ya ce kungiyar

Shugaban kasar Lebanon Josept Aoun ya bayyana cewa gwamnatinsa tana son ta maida makamai a kasar Lebanon karkashin ikon hukuma kadai. Aoun ya ce kungiyar Hizbullah tana iya shiga harkokin siyasa na kasar Lebanon amma makamai na gwamnatin ne kadai.

Jaridar ‘The National Ta Kasar Amurka’ ta n akalto shugaban yana fadar haka a kasar Masar a ganawarsa da tokwaransa na lasar Abdulfattah Assisi a yau Litinin.

Aoun ya kara da cewa yana bukatar taimakon kasar Masar don gano ramukan da ake boye makamai a kasa. Sannan zai yi magana da shugaba Mahmood Abbas na Falasdinawa kan yadda za’a karbe makaman da suke hannun falasdinawa a sansanoninsu na yan gudun hijira da ke Ainul Helwa kusa da garin Saida na kudancin kasar Lebanon.

Da aka tambaye shi dangane da yankunan kasar Lebanon wadanda har yanzun HKI na mamayeda su da fursinonin kasar Lebanon da ke hannun HKI, Aoun ya ce yana magana da Amurkawa, don ita kadai ce za su takurawa HKI ta fice daga kasar Lebanon ta kuma saki yan kasar wadanda suke hannun HKI.

Kafin haka dai kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa ba zata taba rabuwa da makamakanta sai randa babu wata kasa Isra’ila a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments