Donald Trump da ya amince da Qudus a matsayin fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra’ila, shin zai iya dakatar da yakin Gaza kuwa!
Tun farkon yakin neman zabensa, Trump ya tsaya tsayin daka kan haramtacciyar kasar Isra’ila ta murkushe al’ummar Zirin Gaza, kamar yadda ya fada a muhawarar farko ta kafafen yada labarai tsakaninsa da shugaba Biden, kafin Biden din ya janye daga takarar, yana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ita ce take son ci gaba da yakin, kuma dole ne a bar ta ta gama aikinta. Don haka manazarta da masharhanta suke tambayar cewa mane ne ra’ayinsa game da dakatar da yakin Gaza?
Trump ya kuma nuna adawarsa da yunkurin Biden na neman tsagaita bude wuta a Gaza, inda ya nanata fiye da sau daya cewa; Da a ce yana kan karagar mulki da kungiyar Hamas ba ta kaddamar da harin ranar 7 ga watan Oktoba na Ambaliyar Al-Aqsa ba.
Sannan Trump ya yi alkawari a gaban al’umma a lokacin yakin neman zabensa ga Amurkawa Larabawa da Musulmi masu kada kuri’a a kwanakin baya cewa; Idan ya dare kan karagar mulkin Amurka zai dauki matakin kawo karshen yakin Gaza.
A ‘yan watannin da suka gabata, Trump yayi kiran kawo karshen yakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a Gaza, kuma a ‘yan kwanan nan ya fada wa Fira Ministan gwamnatin Isra’ila Benjamin Netanyahu cewa: Dole ne su kawo karshen yakin ta hanyar gama shi cikin sauri, amma dole ne a kawo karshen yakin.