An zabi mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Naim Qassem a matsayin sabon shugaban kungiyar inda zai gaji Sayyed Hassan Nasrallah wanda ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kai a kudancin Beirut a watan jiya.
A ranar Talata ne Majalisar Shura ta Hizbullah, dake yanke shawara ta kungiyar ta nada malamin mai shekaru 60 a kan mukamin.
Sheikh Qassem wani jigo ne a kungiyar Hizbullah, wanda ke rike mukamin mataimakin sakatare janar na kungiyar tun shekara ta 1991.
An nada shi mataimakin babban sakatare a karkashin marigayi babban sakataren kungiyar, Abbas al-Musawi, wanda wani harin helikwafta na Isra’ila ya kashe a shekarar 1992, kuma ya ci gaba da kasancewa a matsayin lokacin da Nasrallah ya zama shugaba.
Harkar siyasarsa ta fara ne a cikin kungiyar Amal ta kasar Lebanon, wadda aka kafa a shekarar 1974. Ya bar Amal a shekarar 1979, bayan juyin juya halin Musulunci na Iran.
Ya halarci tarukan da suka kai ga kafa kungiyar Hizbullah a shekarar 1982.
Sheikh Qassem ya dade yana daya daga cikin manyan masu magana da yawun kungiyar Hizbullah, inda ya yi hira da manema labarai da dama.
An haife shi a shekara ta 1953 a gundumar Basta Tahta ta Beirut, kuma asalinsa danginsa sun fito ne daga garin Kafar Fila da ke lardin Nabatie na kudancin Lebanon.