Sharhi : Jawabin Aragchi A Taron Tunawa Da Kharrazi

Assalamu alaikum, sharhin bayan labarammu zai yi magana kan jawabin ministan harkokin wajen kasar Iran don girmama shahida Kamal Kharrazi, tsohon ministan harkokin wajen kasar.

Assalamu alaikum, sharhin bayan labarammu zai yi magana kan jawabin ministan harkokin wajen kasar Iran don girmama shahida Kamal Kharrazi, tsohon ministan harkokin wajen kasar. Wanda ni tahir amin zan karanta.

///…Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi, ya bayyana cewa JMI tana neman zaman lafiya da kekyawar zamantakewa da kasashe makobta, tare da karfafa cewa, zaman lafiya tana samuwa ne a yankin yammacin Asia ne kadai idan kasashen yankin da kansu ne suka samar da shi da kansu, ba tare da shishigi na kasashen waje ba, kasashen suke daga wajen yankin.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na gwamnatin kasar Iran, ya nakalto Aragchi yana fadar haka, a ranar Lahadi 25 ga watan Octoba na shekara ta 2026, a lokacinda yake jawabi a wani taro na musamman a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran da ke nan Tehran, saboda girmama Shahid Kamal Kharrazi, da kuma bayyana gudumawarsa wajen karfafa al-amuran diblomasiyya na JMI da kuma karfaf jami’an diblomasiyyar Kasar.

Har’ila yau a taron ne ministan ya kaddamar da sashen kayakin tarihi da ajiye takardu masu muhimmanci na ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran wanda aka sanyawa suna, Shahid Kharrazi. Har’ila yau ministan yayi amfani da taron don kaddarmar da dakin karatu na ma’aikatar wanda aka kammala gyransa bayan da hare haren da Amurka da HKI a farkon wannan shekarar suka lalata shi.

Shahid Kamal Kharrazi ya yi shahadi a ranar 9 ga watan Afrilun shekara ta 2026, sanadiyyar raunukan da ya ji a hare haren Amurka da HKI kan gidansa a yakin da suka fara a ranar 28 ga watan Fabrayru na wannan shekarar. Banda haka, shahid Kharrazi shi ne shugaban kwamin na musamman kan tsara yanda za’a tafiyarda al-amuran harkokin waje a ma’aikatarsa, har’ila yau shi ne shugaban masu kwamitin masu bawa jagoran juyin juya halin musulunci shawara a kan al-amuran harkokin waje. Kuma shi ne shugaban kwamitin tallafawa harkokin gudanarwa a ma’aikatar harkokin wajen kasar, sannan tsohon ministan harkokin wajen kasar JMI.

A jawabinda nasa Aragchi ya tunatar da masu sauraro jawabin shahid Kharrazi a taron fahintar juna tsakanin Iran da kasashen larabawa, a cikin watan Mayun shekara ta 2025 a birnin Doha na kasar Qatar, watanni kafin HKI ta farwa kasar Iran da kallafeffen yaki na kwanaki 12, sannan kasa da shekara guda kafin kallafeffen yakin da muke ciki wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar.

A taron Shahid Kharrazi, ya jaddada matsayin JMI na cewa, nasara da kuma tsaron yankin yammacin Asiya ya dogara ne kadai kan gudumawar dukkan kasashen wannan yankin ba tare da samuwar sojojin kasashen waje a cikinsa ba.

Ministan ya ce: Fahintar da shahid Kharrazi ya bayyana kafin yake yake biyu wadanda aka dorawa JMI, har hanzun sune matsayi na asasi ga JMI dangane da samuwar zaman lafiya da tsaro a wannan yankin. Wato kasashen yankin ne kadai zasu iya samar da zaman lafiya a yankinsu da kansu, ba tare da dogaro ko gayyatar sojojin kasashen waje zuwa yankin ba. JMI a shirye take ta taimaka wajen cimma wannan maufar kuma a shirye take ta shiga tattaunawa mai zurfi da dukkan kasashen yankin kan al-amarin’. Ya kara karfafa maganar cewa, Iran tana bukatar zaman lafiya da dukkan kasashe makobta a wannan yankin, a kuma rayu tare cikin aminci.

Ministan yace: Tsarin makobtaka a wajemmu shi ne, zaman lafiya tare da makobtammu. A baya haka muke, a yanzun ma wannan shi ne matsayimmu, kuma nan gaba ma haka zamu kasance da makobtammu. Yace, saboda haka ya zama dole, nemo al-amura da muka yi tarayya a cikinsu, don warware matsalolin tsarommu da kuma na yankimmu, tare da gudumawar dukkan kasashen yankin, ba tare da shishigin sojojin wata kasa daga waje ba.’ .

A fadin ministan harkokin wajen kasar Iran, yake yake guda biyu da aka dorawa JMI daga shekara ta 2025, ya tabbatar da cewa samuwar sansanonin sojojin Amurka a cikin kasashen yankin, ba lamuni ne na zaman lafiya ga kasashen ba. Yace wadan nan yake yake biyu sun kara tabbatar da cewa, dogaron da wasu kasashen yankin suka yi kacokab da kariyar sojojin kasashen waje, ko kuma shigowarsu yankin ya tabbatar da gazawarsu wajen samar da abinda ake bukata.

Sansanonin sojojin Amurka a cikin wasu kasashen yankin basu samar da zaman lafiya da tsaro ga kasashen ba. Sai dai akasin haka, wato samuwarsu da kans, ya zama rashin tsaro da zaman lafiya. Da farkon daga wadan nan sansanonin sojojin Amurka ne Amurka da HKI suka farwa kasar Iran da yake yake, da haka kuma suka zama barar JMI a maida martanin da suka biyu baya.

Aragchi y ace, da wannan kuma, maimakon su zama sandiyyar samar da tsaro a kasashen, sai suka zama sune musabbin karin rashin tsaro a kasashen da kuma yankin.

Ministan ya tunatar da masu sauraro kan cewa, ainihin manufar tahowar sojojin kasashen waje cikin yankin, ba don karesu su da kuma samar da zaman lafiya ba, sai dai sun shigo yankin ne don kare HKI, wanda shi ma sun kasa. Yace HKI ita ce babbar mai samar da fitina da tashin hankali a yankin.

Daga karshen yace: yakin kwanakin 40 ya sauya al-amura da dama a yankin, kuma ba zasu sake komawa kamar yanda suke a da ba, daga ciki har da mashigar ruwa ta Hurmuz.

Karshen sharhin Kenan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted