Babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa Iran za ta yi amfani da dukkan karfinta wajen kare shirinta na nukiliya cikin lumana.
A yayin wata ziyara da ya kai wani baje kolin da ke nuna sabbin nasarorin da aka samu a masana’antar nukiliya a hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) a ranar Litinin din nan, Ali Shamkhani ya sake nanata gaskiyar shirin nukiliyar Iran da kuma yadda kasar ke bin ka’idojin kasa da kasa.
“Iran ba ta taba neman makaman nukiliya ba kuma ba za ta taba yin hakan ba,” in ji shi. “Duk da haka, tana kare hakkinta da dukkan karfinta.”
Shamkhani ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kuduri aniyar kare muradun al’ummar Iran daga wuce gona da iri na manyan kasashen duniya, wadanda suka yi watsi da alkawuran da suka dauka.