Senegal ta sake gano wasu shaidu kan kisan  gillar da aka yi a lokacin mulkin mallaka

Masana kayan tarihi a Senegal sun gano sabbin shaidu na kisan gillar da aka yi a lokacin mukin mallakar Faransa a kasar a shekarar 1944,

Masana kayan tarihi a Senegal sun gano sabbin shaidu na kisan gillar da aka yi a lokacin mukin mallakar Faransa a kasar a shekarar 1944, a matsayin wani bangare na kokarin da gwamnati ke jagoranta na gano gaskiya game da batun kisan da sojojin Faransa suka yi a kasar da ke yammacin Afirka a lokacin da ake cikin yakin duniya na biyu.

Makabartar sojojin Thiaroye, wacce ke kusa da babban birnin Dakar, a halin yanzu ita ce wurin bincike da aka yi fafakeken rami domin tono kayan tarihi da nufin gano gawarwakin sojojin da ake zargin sojojin mulkin mallaka na Faransa sun kashe su a ranar 1 ga Disamba, 1944.

Lamarin ya faru ne bayan da aka kawo kusan sojoji 1,600, waɗanda da yawa daga cikinsu ba a jima da ‘yantar da su daga bauta a Jamus ba zuwa sansanin tsare mutane a Thiaroye, kuma suka fara zanga-zangar nuna rashin amincewa da kin biyan su  albashi da rashin daidaito.

Sojojin Faransa sun buɗe wuta kan mutanen, amma an daɗe ana jayayya kan adadin waɗanda suka mutu da kuma ainihin yanayin da aka kashe su. Bayanan mahukunta na zamanin mulkin mallaka sun yi iƙirarin mutuwar mutane 70, amma masu bincike na Senegal sun ce adadin na iya kaiwa tsakanin 300 zuwa 400.

Masana kayan tarihi sun tono kaburbura bakwai daga cikin rukunin farko na mutane 34, suna gano cikakkun kasusuwa da kuma ɓangarorin da suka rage na gawawarkin mutane. A cewar masanin kayan tarihi Moustapha Sall, an gano ɗaya daga cikin kasusuwan wata gawa da harsashi ya makale kusa da sashen zuciya. Wasu kuma sun nuna alamun munanan raunuka, sannan kuma an gano wasu gawawwaki da sarƙoƙin ƙarfe a ƙafafunsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments