Jam’iyyar PASTEF, a Senegal, ta sanar da korar shugaban kasar Bassirou Diomaye Faye daga jam’iyyar wanda ya kara fiddo a fili rashin jituwar dake tsakaninsa da tsohuwar jam’iyyarsa.
A wata sanarwa da ta fitar Jam’iyyar ta sanar da korar mambobinta 32, ciki har da shugaban kasar.
Daga cikinsu kuma akwai ministoci shida daga Pastef wadanda suka yanke shawarar ci gaba da zama a gwamnati bayan korar Ousmane Sonko daga mukamin FiraMinista a watan Mayu.
Wannan shawarar ta zo ne a daidai lokacin da ake samun rarrabuwar kawuna tsakanin Bassirou Diomaye Faye da Ousmane Sonko, wadanda suka kasance abokan hamayya a lokacin zaben shugaban kasa na watan Maris 2024.
A watan Yulin da ya gabata, shugaban kasar ya sanar da kirkirar jam’iyyarsa ta siyasa, mai suna Kiiraay a ranar 25 ga Yuli.
Sanarwar ta zo ne yayin da rikici tsakanin Bassirou Diomaye Faye da tsohon mai ba shi shawara, Ousmane Sonko, ya kara ta’azzara a cikin ‘yan watannin nan.
Bayan an sake zabensa a matsayin shugaban jam’iyyar Pastef, Sonko ya bayyana a ranar 14 ga Nuwamba, rabuwar da tsohon abokin tafiyarsa ta tabbata.
Tsohon firaministan ya kuma nuna cewa bai yi wata mu’amala ta zahiri ko ta waya da shugaban kasa ba tun watan Yuni, a daidai lokacin da wasu muryoyi da dama suka yi kira da a yi taro tsakanin mutanen biyu don ci gaba da tattaunawa.