Sakataren Majalisar Koli Ta Tsaron Kasar Iran Ya Isa Kasar Rasha

A yau Talata ne babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya isa birnin Saint Petersburg na kasar Rasha da zummar halartar taron tsaro

A yau Talata ne babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya isa birnin Saint Petersburg na kasar Rasha da zummar halartar taron tsaro na kungiyar Brics.

Taron wanda shi ne irinsa karo na 12 a karkashin kungiyar Brics, ya kunshi shugabannin hukumomin tsaro ne na kasashen da suke mambobi.

Bugu da kari da akwai ministocin tsaro na kasashe fiye da 100 da suke halartar taron na Rasha, inda daga Iran babban sakataren hukumar tsaron kasar, kuma wakilin jagoran juyi a majalisar tsaron kasar Ali Akbar Ahmadiyan wanda yake  halarta.

A tsawon lokacin kasantuwarsa a kasar ta Rasha, Ahmadiyan zai yi ganawar bayan fage da takwarorinsa na duniya da suke halartar taron domin bunkasa alaka ta fuskar tsaro da kasashen nasu.

A kowace Shekara kasar Rasha tana shirya wannan irin taro na tsaro a cikin daya daga biranenta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments