Search
Close this search box.

 Sakataren Kungiyar Kasashen Larabawa Yayi Tir Da ci Gaba Da Kai Hare-haren Isra’ila A Gaza.

A wata ganawa da aka yi tsakanin babban sakataren kungiyar hadin kan kashen larabawa Ahmad Abul Gaith da manzon musamman na majalisar dinkin duniya Frankchzka

A wata ganawa da aka yi tsakanin babban sakataren kungiyar hadin kan kashen larabawa Ahmad Abul Gaith da manzon musamman na majalisar dinkin duniya Frankchzka Albaniz kan alamuran falasdinu ya bayyana cewa  Isra’ila tana kokarin toshe sautin duk wani dake Magana kan kisan kiyashinta a Gaza.

Abul Gaith  ya kara da cewa:  Isra’ila tana aikata laifukan yaki  da gangan da nufin hukunta mazauna yankin tare da take hakkokin Falasdinawa da ke zaune a cikin kasashensu, kuma babu  wani ma’auni da za a iya kiran laifukan Isra’ila a matsayin  kuskure.

Ashraf kadare kakakin ma’aikatar lafiya ta yankin falasdinu a yankin gaza da yake bayani game da hare haren da isra’ila takai a cibiyoyin shan magani a yankin gaza ya ce Isra’ila ta rusa dukkan asibitocin dake gaza baki daya, haka zalika da gangan take kashe yara kanana a Gaza, inda ya zuwa yanzu ta kashe yara dubu 13 da 800 .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments