Sakamakon Jin Ra’ayin Isra’ilawa: Kashi 66% Na Goyon Bayan Kawo Karshen Yakin Gaza

Wani saksmkon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar dimokuradiyya ta Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kashi 66 cikin 100 na Isra’ilawa sun yi imanin

Wani saksmkon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar dimokuradiyya ta Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kashi 66 cikin 100 na Isra’ilawa sun yi imanin cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen yakin Gaza, tare da bayyana hadarin da fursunoni ke fuskanta.

Wannan adadi na kashi 66% ya karu da kashi 13% a kan sakamakon da aka fitar a shekara guda da ta gabata lokacin da aka yi musu tambaya iri ɗaya.

Sakamakon  ya kuma nuna cewa kashi 45% na Isra’ilawa sun yi imanin cewa ya kamata Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya yi murabus nan da nan kafin karshen yakin, tare da dora masa alhakin abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Sakamakon ya nuna cewa kashi 19% na Isra’ilawa suna son Netanyahu ya yi murabus, saboda wannan dalili, amma bayan yakin.

Wadannan ra’ayoyin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Isra’ila musamman iyalan fursunoni da suke nean kawo karshen yakin domin ceton ‘yan uwansu da aka yi garjuwa da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments