Shugaban Iran Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Na Goyon Bayan Kungiyoyin Gwagwarmayar

Zababben shugaban kasar Iran ya aike da saƙo ga ‘yan gwagwarmaya  da a cikin ya jinjina musu kan kare kimar dan Adamataka da suke yi

Zababben shugaban kasar Iran ya aike da saƙo ga ‘yan gwagwarmaya  da a cikin ya jinjina musu kan kare kimar dan Adamataka da suke yi

Zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya mayar da amsar sakon taya murna da jagororin ‘yan gwagwarmaya a yankin Gabas ta Tsakiya suka aika masa, inda a cikiPezeshkian ya jaddada cewa, Iran a ko da yaushe tana goyon bayan gwagwarmayar kare kai daga makircin yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da suke yi kan al’ummar yankin da nufin cimma munanan manufofinsu na mamaya, yana mai jaddada cewa: Wannan goyon baya zata ci gaba da karfi domin karfafa juriyar al’ummar yankin da suke yi na mayar da martani kan bakar siyasar yahudawan sahayoniyya.

Zababben shugaban na Iran ya kara da cewa: Goyon bayan gwagwarmayar ya samo asali ne daga manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, karkashin jagorancin marigayi Imam Khomeini (Allah Ya kara masa yarda) da kuma umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Sayyid Ali Khameine’i, kuma Iran zata ci gaba da mara baya ga gwagwarmaya da dukkanin karfinta.

Pezeshkian ya ci gaba da cewa: Yana da tabbacin cewa goyon bayan kungiyoyin gwagwarmaya a yankin ba zai bar wannan haramtacciyar kasa ta ci gaba da aiwatar da munanan manufofinta na tada fitina da ta’addanci kan al’ummar Falastinu da ake zalunta da sauran al’ummomin yankin ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments