Sabon Ministan Tsaron Iran Ya Ce: Babban AIki Da Zai Sa A Gaba Shi Ne Kalubalantar ‘Yan Shayoniyya

Ministan Tsaro na Iran ya bayyana cewa: Daya daga cikin abubuwan da kasarsa ta sanya a gaba shi ne fuskantar hatsarin yahudawan sahayoniyya da ta’addanci

Ministan Tsaro na Iran ya bayyana cewa: Daya daga cikin abubuwan da kasarsa ta sanya a gaba shi ne fuskantar hatsarin yahudawan sahayoniyya da ta’addanci

Kakakin Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Shura ta Musulunci, Ibrahim Reza’ei, ya bayyana cewa: Hujjatul-Islam Ismail Khatib, dan takarar da zai karbi mukamin kula da tsaro a sabuwar majalisar ministocin Iran ya sanar da cewa: Wannan ma’aikatar tana fuskantar wasu hukumomin leken asirin kasashen waje 53, da suke aiki bisa tsari na yakar kasar ta Iran, kuma ya jaddada cewa daya daga cikin abubuwan da ma’aikatar ta sa a gaba shine tunkarar ‘yan sahayoniyya da ta’addanci.

Wannan ya zo ne a cikin wata sanarwa da Reza’ei ya yi wa manema labarai a ranar Litinin game da halartar Hujjatul-Islam Khatib, ministan tsaro a gwamnati ta 13 da kuma dan takarar da zai karbi mukamin na tsaro a sabuwar majalisar ministocin kasar, a yayin zaman taron na kasa, zaman taron kwamitin tsaro da harkokin waje, wanda aka gudanar a ranar Litinin don bayyana tsare-tsare da shirye-shiryensa bayan karbar ragamar wannan matsayi da kuma amsa tambayoyin Majalisar Shawarar Musuluncin Kasar.

Kakakin kwamitin tsaron kasa da manufofin harkokin waje a majalisar shawarar ya kara da cewa: Hujjatul-Islam Khatib ya tabbatar da cewa makiya sun zuba hannun jari mai yawa a fagen kutsa kai a harkokin Iran, kuma daya daga cikin abubuwan da ma’aikatar tsaron kasar ta Iran ta sa gaba shi ne fuskantar yahudawan sahayoniyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments