Rikici Tsakanin Fira Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Da Ministan Gwamnatinsa

Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ministan tsaron haramtacciyar kasar suna zargin junansu kan fallasa asirin gwamnatinsu Jam’iyyar Likud, karkashin jagorancin Fira Ministan gwamnatin

Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ministan tsaron haramtacciyar kasar suna zargin junansu kan fallasa asirin gwamnatinsu

Jam’iyyar Likud, karkashin jagorancin Fira Ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, ta yi nuni da cewa: Ministan Tsaron Cikin Gidan haramtacciyar kasar Isra’ila Itamar Ben Gvir, yana tona asirin tattaunawan sirri da matakan sirri da majalisar ministocin tsaro da siyasar haramtacciyar kasar Isra’ila suka gudanar, bayan da rahotannin kafafen yada labaran yahudawan sahayoniyya suka fitar.

A cikin sanarwar da Jam’iyyar Likud ta fitar ta ce: Labaran sirri da ake yadawa kan gwamnati suna cike da kura-kurai, kuma fira Minista Netanyahu ya gaya wa minista Ben Gvir magana mai sauƙi cewa: Duk wanda ke son zama abokin tarayya a majalisar yaƙi dole ne ya tabbatar da cewa baya tona asirin gwamnati ko fallasa tsare-tsare na musamman da ake tattaunawa a majalisar.

A martanin da jam’iyyar Ben Gvir ta Yahudawa Power-Otzma Yehudit ta mayar ta sanar da cewa: Tana goyon bayan dokar da ta bukaci mambobin majalisar yakin su kasance masu fasahar gano karya.

Ben Gvir dai memba ne a majalisar ministocin tsaro amma baya cikin karamar majalisar ministocin yaki, kuma yana kokawa kan cire shi da Netenyahu ya yi daga cikin Majalisar yaki a haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments