Rezaei : Lokaci Ya Yi Na Amurka Ta Amince Da Sharuddan Iran

Janar Rezaei ya riga ya bayyana cewa Tehran ta isar da sharudda bakwai ga gwamnatin Amurka.

Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Manjo Janar Mohsen Rezaei, ya shaida cewa lokaci ya yi da Amurka cewa ya kamata ta amince da ka’idoji bakwai da Tehran ta gindaya da kuma daina kirkirar bayanan karya game da tattaunawar da ake yi.

A cikin wani sako a shafukansa na sada zumunta, Rezaei ya tabbatar da cewa yakin da Washington ta kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya riga ya gurgunta gwamnatin Amurka, a yayin da Fadar White House ta shiga damuwa.

Sharuddan, wadanda aka sanar da Washington a hukumance a karon farko a watan Satumba ta hannun Qatar da sauran masu shiga tsakani na yankin, sun hada da kawo karshen rikici a dukkan fannoni a Lebanon, Gaza, da Yemen – sakin kadarorin Iran da aka daskarar, kawo karshen shingen da akayi wa tashohin jiragen ruwa ba bisa ka’ida ba gaba daya, cire takunkumin tattalin arziki da siyasa, janye sojojin ruwa da na sama na Amurka daga yankin, biyan diyya ta yaki, da kuma kawo karshen barazana da cin zarafi.

Iran ta jaddada cewa dole ne Washington ta cika sharuddan bakwai don ba da damar sake fara tattaunawar diflomasiyya, saboda tattaunawar da ke tsakanin bangarorin biyu a halin yanzu ta tsaya cak saboda yakin da ake yi da Iran.

Janar Rezaei ya riga ya bayyana cewa Tehran ta isar da sharudda bakwai ga gwamnatin Amurka don bude duk wata tattaunawa, yana mai bayyana sakon a matsayin “bayyananne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted