SABON TSARIN DUNIYA

Wadanne canje-canje ne shan kayin Amurka da Isra’ila a yakinsu da Iran zai kawo ga tsarin duniya?2A cewar masu sharhi da yawa, Amurka da Isra’ila

Share

Yakin da ke gudana ya nuna cewa karfin juriya da dogaro da kai na iya sauya akalar siyasa a duniya. Tambaya ita ce: shin wannan zai kawo sabon tsari ko kuwa tsohon zai ci gaba?

Wadanne canje-canje ne shan kayin Amurka da Isra’ila a yakinsu da Iran zai kawo ga tsarin duniya?
2
A cewar masu sharhi da yawa, Amurka da Isra’ila ba su cimma burinsu ba kuma ba su da wani sabon zaɓi na kawo wani sabon canji a yakin.
3
Ba su sami damar kifar da Jamhuriyar Musulunci ba, ba su iya bude mashigar Hormuz ba, ba su iya rusa makamai masu linzami na Iran ba, kuma ba su iya raunana matsayin kasar a yankin ba.
4
Idan wannan yanayi ya ci gaba, shan kayin Amurka da Isra’ila a yakin shine zato mafi rinjaye.
5
Tambayar dam asana ke yi ita ce, ko tasirin wannan yakin zai haifar da wani sauyi a tsarin yankin gabas ta tsakiya da ma duniya?
6
A zahiri dai bisa la’akari da abubuwan da suke bayyana a kafofin yada labarai da shafukan sada zumunta, mutane a sassa daban-daban na duniya suna bin kadun lamarin sosai.
7
A Latin Amurka, yankin da aka dade ana daukarsa a matsayin w mai riko da tsoffin al’adu na gargajiya, suna da gogewa matuka kan yadda cutarwa da matsin lamba na ‘yan mulkin mallaka ke yin tasiri wajen rusa zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma.
8
A gabas at tsakiya, kasashen Larabawa da yawa sun gani a zahiri kan cewa, dogaro da kuma bin da manufofin Washington bai kawo musu tsaro ba, domin kuwa ba shi ne burinta ba, manufar ita ce mayar da su tamkar shanu da za ta rika tatsa.
9
A Turai, akwai alamun canji a cikin tunanin jama’a har ma da wasu manyan ‘yan siyasa a yanzu fiye da kowane lokaci a baya, inda suke jaddada bukatar samun ‘yancin siyasa da rage dogaro da manufofin Amurka.
10
A nahiyar Afirka, kasashen da suka kasance karƙashin tasirin kasashen ketare a tsawon shekaru, yanzu wasu daga cikinsu suna neman a rage ikon wadannan kasashe, domin kasashen Afirka su dogara da kansu da kuma arzikinsu na cikin gida.
11
A irin wannan yanayi, nasarar da aka samu daga tsayin daka da juriya na iya zama abin koyi mai ban sha’awa ga sauran kasashe da al’ummomi.
12
Akwai kyakkyawan misali da ke tabbatar da cewa juriya da dogaro da kai a cikin gida na iya share fagen yin watsi da dogaro da kasashen ketare.
13
Mene ne naku tunanin? Shin wani sabon sauyi ne za a samu a duniya? Shin wasu canje-canje za su iya faruwa a cikin tsarin cibiyoyin kasa da kasa da kuma bangarorin da ke da ruwa da tsaki a kasashen duniya? Amsar ta dogara ne da abubuwan da za su faru a cikin kwanaki ko watanni masu zuwa.