Yunkurin sake tayar da tarzoma

1 Ku kai wa ‘yan sanda hari, ku fito kan tituna da makamai 2 Wannan wani bangare ne na sakon da Reza Pahlavi ya aike

Share

Hoton tarzoma inda mutane da jami'an tsaro ke gaba da juna a titi

1

Ku kai wa ‘yan sanda hari, ku fito kan tituna da makamai

2

Wannan wani bangare ne na sakon da Reza Pahlavi ya aike wa mutanensa masu dauke da makamai a cikin Iran.

3

Sakon da ta wata fuska yana nuni da cewa yana da alaka kai tsaye da abin da ya faru watanni biyu da suka gabata a Iran.

4

Amma saboda me? Domin fahimtar hakan dole ne mu dan koma baya kamar watanni biyu da suka gabata a lokacin tarzomar watan watan Janairun 2026.

5

A lokacin Pahlavi ya bukaci mutanensa da su fito kan tituna domin su kifar da gwamnati. A wannan lokacin ne Donald Trump ya ce zai kawo wa Iran hari domin taimakon masu zanga-zanga.

6

Amma a mataki na kasa da kasa zanga-zanga ba zata zama dalili na aiwatar da abin da aka shirya ba, dole ne a kirkiro wani abu domin nuna cewa an yi kisan jama’a.

7

Kuma a kan haka ne aka kirkiro batun kisan mutane dubu 40 aka yi ta yadawa a kafofin yada labarai.

8
Adadi ne mai tayar da hankali, kuma a haka aka yi ta yada wa duniya duk da cewa babu wani dalili da ke tabbatar da hakan, har zuwa lokacin da gwamnatin Iran ta fitar da jerin sunayen mutane 3,117 da suka mutu.

9

Babu wata kafar yada labarai wadda ta iya kara ko da sunan mutum daya ne a kan adadin da gwamnati ta fitar.

10

Koma dai yaya lamarin yake, manufar Isra’ila da dan gidan Shah da magoya bayansu a fili take.

11

Cewa duk abin da ya faru tsararren shiri ne, aiki ne na ta’addanci da makamai, domin kuwa fiye da mutane 2,000 da aka kasha jami’an tsaro ne da mutanen gari.

12

Ku tabbas suna wani shiri makamancin hakan a nan gaba a biranen kasar Iran.

13

Shi ma kuma kamar na bayansa mutanen kasar masu kishi za su sake fitowa domin rusa duk wani makirci da aka kitsa a kan kasarsu.