“Farah Abu Ayyash”

"Na yi kuka a dukkanin darare. Ƙwari suna cizon jikina da fuskata gaba daya." Wannan ita ce ruwayar 'Farah Abu Ayyash,' wakiliyar kamfanin dillancin labaran

Share

Wata mace tana zaune a cikin ɗaki mai duhu kamar kurkuku, tana kallon haske daga taga mai sanduna, yanayin yana nuna damuwa da tsarewa.

1

“Na yi kuka a dukkanin darare. Ƙwari suna cizon jikina da fuskata gaba daya.” Wannan ita ce ruwayar ‘Farah Abu Ayyash,’ wakiliyar kamfanin dillancin labaran Tasnim, yadda ta kasance a cikin kurkukun Isra’ila.

2

Farah Abu Ayyash, ‘yar jarida ‘yar Falasɗinu ‘yar shekara 25, tana tsare tun daga 6 ga Agusta, 2025.

3

An kama ta a wani samame cikin dare a gidanta da ke ‘Beit Ommar,’ kuma bayan an kai ta wurare daban-daban ana tsare da ita, ta fi kwanaki 200 tana tsare a gidan kason Damon.

4

Wane Laifi ake zarginta da aikatawa? Laifin Shi ne bayar da rahotanni kan yanayin rayuwar Falasdinawa a Yammacin Kogin Jordan.

5

Bisa ga wasu rahotanni, Farah a lokacin da take tsare, a farkon kwanakin da aka kama ta, ta shafe kwanaki 15 cikin matsanancin hali na yunwa, kuma an sha yi mata tambayoyi akai-akai.

6

Gidan kason Damon, inda take tsare a halin yanzu, yana a wani yanki mai tuddai da ke kudancin Haifa. A cikin wannan gidan yarin, akwai mata Falasdinawa kusan 78 da ake tsare da su.

7

A bisa bayanan lauyoyi, babu wata hanyar samun rediyo, talabijin, littattafai, ko tuntubar iyalai. Ana buɗe tagogin ɗakunan kurkuku da gangan da dare, kuma ana hana fursunonin abubuwan dumama daki.

8

Sa ido ta hanar kyamarori a cikin sa’o’oi 24 a kowace rana, har ma da ɗakunan jiyya, ba su da wani bambanci da sauran bangarori na wannan kurkuku.

9

Rahotanni sun ce ana bincika jikin fursunoni ta hanyoyi na cin zarafi da keta hurumi.

10

Bayanan da aka wallafa suna hakaito irin halin da Farah take ciki. Tun daga lokacin kama ta, an sha mayar da ita tsakanin gidajen yari irin su Moskobiya, Ayalon, da Damon.

11

A cewar lauyanta, ta fuskanci yanayi na matsi da kuntata, tare da tsare ta a dakunan karkashin kasa, da yanayi na rashin tsafta, hana ta tufafi da kayan bukatar rayuwa, da kuma watsi da yanayin jikinta. Farah Abu Ayyash kuma ta sheda wa lauyanta cewa: A wurin da ake tsare ita, an buga kanta da bango, an ɗaure ta da sarƙoƙi, kuma an matsa mata lamba domin ta sumbaci tutar Isra’ila.

12

Bisa kididdiga a hukumance, sama da ‘yan jarida Falasdinawa 30 ne ake tsare da su. Haka kuma a shekara ta 2024, an bayar da alkalumma na ayyukan cutarwa sama da 25,000 kan Falastinawa da ake tsare da su.

13

Kama Farah yana a cikin wannan tsari: wato kame mutanen da suke bayar da rahotanni da bayanai kan rayuwar Falastinawa da hakikanin abubuwan da suke faruwa.

14

Daga ranar 7 ga Oktoba, 2023 zuwa yanzu, kimanin ‘yan jarida 300 ne Isra’ila ta kashe a Falasɗinu, Lebanon, da Iran. Kuma wannan lamari ya sa aikin jarida ya zama mafi haɗari da kashi 59.5% ga ‘yan jarida a fadin duniya a shekara ta 2025.

15

Bisa ga dokokin ƙasa da ƙasa, ‘yan jarida a wuraren yaki ana daukar su farar hula ne. Mataki na 79 na doka ta Farko a cikin Yarjejeniyar Geneva da kudurorin Kwamitin Tsaron MDD sun fayyace cewa dole ne a kare ‘yan jarida, ba a tsare su, ko wulakanta su, ko gajiyar da su, saboda aikinsu na watsa labarai.