Tattaunawar Iran da Amurka lamari ne mai sarkakiya, domin kuwa Iran tana da masaniya da gogewa game da tattaunawa da Amurka, da kuma abubuwan da suka faru a baya, wannan ne yasa take yin taka tsan-tsan da kuma sara tana duba bakin gatari, a lokaci guda kuma tana yin riko da hakkokinta, yayin da Amurka take Kallon wannan tattaunawa ta hanyoyi daban-daban, da suka hada da farfaganda ta siyasa, da kuma neman suna da nuna iko.