A cikin kasa da wata guda, Kasar Siriya ta nunawa duniya fuskokinta biyu, masu matukar sabawa juna.Fuska ta farko, shugaban kasa wanda yayi suna a cikin ayyukan ta’addanci, sanye da kwat da wando, yana cewa zai rungumi Isra’ila. Fuska ta biyu kuma ita ce, sai ga fadar shugaban kasa da ke Damascus wanda ta zama kofai, hayaki na tashi a cikinta.