Wata tambaya mai matukar muhimamnci da masana da kuma masu amfani da shafukan zumunta suke yi ita ce: Ta yaya Iran ta yi tsayin daka a gaban kasashe masu makaman nukiliya.
2
Ta yaya a tsawon shekaru 47 matsin lamba da takunkumai na tattalin arziki ba su iya karya kasar ba? Domin amsa wannan tambaya dole ne a yi ishara da abubuwa biyu: akida ta addini, da kuma tsohon tarihi, ta fuskar addini fiye da kashi 99 cikin dari na mutanen kasar musulmi.
4
Ta wannan fuskar za a iya fahimtar cewa manzon Allah ba wai kawai wani mutum ne da aka yi a tarihi, domin kuwa abin da ya kafa yana nan daram.
5
Misali na juriya da sadaukarwa ta manyan mutane a tarihi da suke yin koyi da su, kamar irin su Imam Ali da Imam Hussain.
6
Baya ga haka kuma tsohon tarihin Iran da iliminta ba abu ne boyayye ba.
7
Suna da imanin cewa sadaukarwa domin tabbatar adalci da kare gaskiya abu ne da ya zama wajibi a cikin rayuwa.
8
Yin galaba a kan mai akida da kuma irin wannan tunanin yana da wahalar gaske.
9
Amma a bangaren samun nasara ko akasin hakan, a wurinsu duk nasara ce, bisa tarihinsu na dubban shekaru sun sha yin gwagwarmaya da manyan daloli kamar yadda ya tabbata a tarihi.
10
Kafin zuwan addinin muslunci sun yaki babbar daular Rom kuma sun yi nasara a kanta, daga baya-bayan nan a lokacin mulkin mallaka sun yi artabu da sojojin Ingila, kamar yadda kuma sun fatattaki sojojin Portugal.
11
Haka nan a lokacin yakin Saddam a kan kasar tare da taimakon Amurka da Burtaniya da Faransa da kuma Tarayyar Soviet da wasu daga cikin kasashen larabawa shekaru biyu bayan samun nasarar Juyi a shekara ta 1979.
12
Iraniyawa suna da akidar cewa, yin sadaukarwa domin kasarsu da al’ummarsu da mutuncinsu, abu ne da yake tare da rayuwarsu, kamar yadda suke koyar da yaransu hakan a makarantu a cikin jumla ta Harshen harshen Farisanci da ke cewa:
13
Idan Iran ba ta da samuwa, Ni ma ba ni da samuwa!