A tsakanin dukkan nazarce-nazarce da matsayar kasashe dangane da Palastinu, Iran tana yin tsokaci ne a kan wata mafita ta daban sabanin sauran ƙasashen. Amma wace mafita ce Iran ke magana a kanta? Shin Iran tana neman wani tsari ne na musamman domin ganin an gudanar da shugabancin Falasdinu a kansa?