1
A wani sabon mataki na dambarwar da ake yi Amurka ta sanar da fara aiwatar da shirin rufe hanyoyin ruwa na Iran, ikirarin da wasu masana suke ganin cewa zai haifar da wasu muhimman tambayoyi da suka hada da cewa: shin Amurka ta dauki wannan mataki ne ba tare da yin la’akari da abin da zai haifar ba ? Ko kuwa ta rufe idonta ne a kan duk abin da zai faru bayan ta killace ruwan Iran?
2
Masanan suna ganin cewa tunanin Karin matsin lamba a kan Iran zai raunana kasar, hakan ya yi hannun riga da abin da yake faruwa a zahiri, mai yiwuwa ma hakan ya kara karfafa kasar.
3
Inda suka bayar da misali da rawar da take takawa a mashigar Hormuz, wanda ya nuna cewa a yanzu kasar ba kawai tana taka rawa a yankin ba ne, har ma tana taka rawa mai tasiri a mataki na duniya.
4
Tekun Farisa da kuma mashigar ruwa ta Hormuz, hanya ce ta fitar da makamashi zuwa kasashen China, India, Pakistan, Iraki, Japan, Koriya ta Kudu, Australia, har ma da kasashen Tarayyar Turai da wasu kasashen duniya da dama.
5
Duk wata matsala da ka iya faruwa a wannan mashiga, to ba za ta takaitu da wata kasa guda daya ba, za ta shafi tattalin arzikin duniya baki daya.
6
Idan aka kalli lamarin ta wannan fuska, to za a fahimci cewa batun ba maganar karfin siyasa ko na sojin Iran ba ne, batu ne da ke nuni da tasirin kasar wanda ya hada gabashi da yammacin duniya, kudanci da arewacin duniya, ta fuskar samar da makamashi da kuma kasuwanci na duniya.
7
Kauda ido daga hakan, yana nufin kauda ido daga mummunan halin da tattalin arzikin duniya zai shiga, matsin lamba a kan kasar yana nufin matsin lamba a kan tattalin arzikin duniya.
8
Abin da zai biyo bayan hakan shi ne: raguwar fitar da danyen mai, hauhawar farashin makamashi da kayan masarufi, matsin tattalin arziki a kan al’ummomin kasashen duniya, daga Turai har zuwa Amurka.
9
Maimakon cutar da wata kasa da nufin raunana ta, za a cutar da kasashe da al’ummomin duniya.
10
Baya ga haka kuma, daukar matakin yin gaban kai daga bangaren Amurka wajen tsayar da jiragen ruwa na kasashen a cikin ruwa na kasa da kasa wanda ba ta da hakki a ciki, hakan zai kara jawo takun saka tsakaninta da kasashen duniya da dama.
11
Tambaya ta karshe ita ce: Shin an yi lissafi sosai kuwa wajen daukar wannan mataki, ko kuwa an dai tafka wani kure ne wanda zai iya jefa duniya cikin wata sabuwar dambarwa?