YAKIN DA BABU DAIDAITO
1
Shin da gaske ne wani jirgin ruwa na dakon mai ya ratsa ta mashigar Hormuz tare da rakiyar jiragen ruwa na Amurka? Mai yiwuwa dai ta wata mashigar ne!
2
Wannan jumlar ta zo ne daga kakakin majalisar dokokin Iran Qalibaf a lokacin da yake bayar da amsa game da ikirari hukumomin Amurka.
3
A rana ta goma a yakin da ake yi a tsakanin bangarorin biyu, Trump da wasu jami’an gwamnatin Amurka sun ce sun rusa rundunar sojin ruwan Iran baki daya, har ma wani jirgin dakon mai ya ratsa ta mashigar Hormuz tare da rakiyar jiragen ruwan yaki na Amurka.
4
To amma abin tambaya shi ne cewa, me yasa har yanzu sojojin ruwan Iran ne suke iko da wannan mashiga?
5
Hakan za ta iya kasancewa ne saboda dakarun na Iran suna da masaniya sosai game da yankin da kuma wannan mashiga fiye da wasu kasashe da ba na yankin ba.
6
Bugu da kari kan hakan, dakarun na Iran sun yi dogon shirin ko- ta- kwana kan faruwar wani lamari makamancin hakan tun tsawon shekaru da suka gabata, baya ga haka kuma suna amfani da makamai masu linzami da ake harba su a kan jeragen ruwa, da wasu abubuwa da suka girke a karkashin ruwa da ake ganin cewa suna da matukar hadari ga manyan jiragen ruwa da suke wuce ta mashigar.
7
To amma shugaba Trump ya fito ya sanar da cewa sun kammala rusa dukkanin karfin rundunar sojin ruwa ta Iran, bayan kai hari kan wasu jiragen yaki na ruwa na kasar ta Iran, a daidai lokacin da wannan rundunar ce kuma take ci gaba da rufe mashigar Hormuz.
8
To ko ma dai yaya lamarin yake, abin da yake faruwa a kasa shi ne yake yin tasiri wajen fayyace makomar yakin, wanda ya shafi dukkanin bangarori na harkokin kasuwar makamshi ta duniya.
9
Abin jira a gani dai shi ne ta yaya duniya za ta fuskanci wannan lamari da kuma daukar matakan kawo karshensa.