DUNIYA A CIKIN WASU ZAMUNA MASU ZUWA

A bisa hasashenku nan da shekara ta 2050 ya duniya za ta kasance? Ya tsarin manufofin da ke tafiyar da duniya zai kasance?

Share

Hoton duniya da ta rabu gida biyu, yana nuna gasa da rikici a tsarin duniya na gaba.

A bisa hasashenku nan da shekara ta 2050 ya duniya za ta kasance? Ya tsarin manufofin da ke tafiyar da duniya zai kasance?
2
Tsarin da ke tafiyar da duniya bayan yakin duniya na biyu tsari ne na jari hujja a bisa mahangar yammacin duniya musamman Amurka, a halin yanzu an fara samun sabani kan wannan mahanga hatta a cikin mambobin kungiyar NATo.
3
Abin da yake a gaban Amurka shi ne tabbatar da manyan manufofinta, kamar dakushe saurin ci gaban China, da kuma abin da take kira da sabon tsarin gabas ta tsakiya, duk da cewa har yanzu ba ta cimma wadannan manufofi ba.
4
Ga dukkanin alamu dai a bisa sabon tsarin duniya, akwai sauye-sauye da suke bijirowa wadanda suke zama karfen kafa ga shirin tabbatar da duniya a kan tsari mai bin mahanga guda daya.
5
A yanzu ana samun wayewa da ci gaban tunani da mahnaga da ke yin karo da mahanga ta jari hujja, tun daga yammacin Asia, har zuwa Latin Amurka, har ma da Turai da arewacin Amurka.
6
Kasar Iran wadda ke da tsohon tarihi na tsarin gudanarwa tun dubban shekaru da suka gabata, a halin yanzu tana daga cikin kasashe masu mahanga wadda ta yi hannun riga da ta jari hujja.
7
Juyin juya hali shi ne ya yi babban tasiri wajen sauya alkiblar kasar wadda a baya ba da jimawa ba ta kasance ‘yar amshin shata ga kasashen yamma.
8
A bisa sabuwar mahangar da aka gina tsarin kasar a bayan juyi, dole ne a bayar da fifiko wajen dogaro da kai da ‘yanci na siyasa, tattalin arziki, tsaro, har ma da sauran batutuwa na zamantakewar al’ummar kasa.
9
Yin tsayin daka a kan wannan manufa yana tattare da sakamako da ya biyo baya, kamar kakaba takunkumai, matsin lamba, har ma da kaddamar da yaki kan kasar Sau uku.
10
Amma Kasar ta mayar da matsin lamba da kalu-bale zuwa wata babbar dama
11
Masana suna da imanin cewa, jajircewa da yin tsayin daka a kan manufa, shi ne babban sirrin nasarorin da kasar ta cimmawa a fagage da dama a cikin shekarun baya-bayan nan.