Tabas ta 2

A ranar 5 ga Afrilu 2026, an tura jiragen sama kirar C-130 guda biyu da wasu kirar Black Hawk guda biyu na Amurka don ceto

Share

Tabas desert, military aircraft and helicopters in sandstorm, dramatic scene

1

Shin wane irin jafa’i ne ya fada wa Amurkawa a cikin kasar Iran?

2

A ranar 5 ga Afrilu 2026, an tura jiragen sama kirar C-130 guda biyu da wasu kirar Black Hawk guda biyu na Amurka don ceto matukin jirgin yakin Amurka F-15 da ya fadi a kasar.

3

Amma dukkan jiragen guda hudu sun bace kuma basu aiwatar da aikin da suke nufin aiwatarwa ba.

4

Kwanaki biyu da suka gabata, an harbo wani jirgin yaƙin Amurka samfurin A-10 da wasu jiragen helikwafta guda biyu.

5

Tabbas, wannan ba shine karon farko ba. Bari mu koma baya tun shekarar 1980; a lokacin aiwatar da abin da suka kira Operation Eagle Claw.

6

Wani samame ne da sojojin Amurka suka shirya don ‘yantar da jami’an diflomasiyyar Amurka 53 a Tehran. Bayan watanni suna shiri, jiragen sama kirar helikwafta 8 da wasu jiragen sama kirar C-130 sun shiga hamadar Tabas.

6

Da farko, jiragen helikwafta uku sun yi rashin nasara wajen aiwatar da aikinsu a asirce, kuma Jimmy Carter ya ba da umarnin a soke aikin.

7

Amma lamarin bai kare a nan ba. Guguwar Hamada ta fara kadawa.

8

A lokacin da suke shirin komawa, wani jirgin sama mai saukar ungulu ya yi karo da wani jirgin. Sojojin Amurka ala tilasta suka bar gawawwakin abokansu da kayan aikinsu a wurin.

9

To me ya faru Sakamakon haka? Mutane 8 sun mutu, jirgin sufuri da helikwaftoci sun kone kurmus, sannan sun bar wasu jiragen helikwafta 5 a cikin hamadar Tabas.

10

Mujallar Time ta rubuta cewa : “Ba guguwar ce kawai matsalar ba; rashin kyakkyawan tsari ne ya jawo musu matsala.”

11

Yanzu kuma a lardin Isfahan an maimaita wani abu makamancin haka da nufin ceto matukin jirgi, wanda shi ma wannan shirin ya fuskanci sakamako irin na shekarun baya.

12

Rushewar shirin baki daya tare da konewar dukkanin jiragen da kuma kasa aiwatar da shirin. Wato Trump ba tare da cikakkiyar masaniya da fahimtar yanayinkasar Iran ba, ya shiga yaki da ita, inda ya jefa kansa a cikin tarkon da ba zai iya fita cikin sauki ba.

14

Don kare kansa, nan da nan ya fara fitar bayanai yana iƙirarin cewa an ceto matukin jirgin Amurka. Amma hotunan da aka fitar sun nuna akasin haka.

15

Me yasa tun daga wancan lokacin a cikin tsawon shekaru 47 babu wani hari kai tsaye da Amurka ta kai wa Iran?

16

Wasu masu sharhi suna cewa, tun daga lokacin suna kallon Iran a matsayin wani wuri mai matukar hadari wanda za a iya fuskantar matsala a cikinsa babu zato babu tsammani.

17