Iraniyawa suna cewa, idan sarrafa wani abu mai amfani yana da wahala me zai hana a yi amfani da haya ta biyu? A cikin irin wadannan dabarun, mashigar ruwa ba kawai hanyoyi ba ne; hanya ce ta shimfida iko da karfi.
2
A yau, an san mashigar ruwa ta Hormuz a matsayin ɗaya daga cikin mahimman wuraren shimfida iko a kan makamashin duniya. Amma gaskiyar magana ita ce tsaron makamashin duniya bai dogara kawai akan Hormuz ba.
3
Baya ga mashigar ruwa ta Hormuz, akwai wata hanya mai mahimmanci wacce ba ta sami kulawa sosai ba: Tekun Maliya.
4
A Tekun Maliya, musamman a mashigar ruwa ta Babul Mandab, akwai ɗaya daga cikin mahimman hanyoyin jigilar mai da kaya zuwa Turai da Afirka. Wannan yana nufin cewa duk wani canji a matsayin wannan hanyar zai shafi kasuwar duniya kai tsaye.
5
Ina ma’anar take? Ba batun maye gurbi ne, muhimmin batun shi ne tabbata da kuma dorewa.
6
Wato kamar yadda Hormuz ke da muhimmanci, haka nan Tekun Maliya yake da nasa muhimamncin.
7
To amma me ya sa yake da muhimmanci? Na farko: bambancin hanyoyin shige da fice a wannan teku da kuma yadda hada bangarori biyu na manyan ruwa na duniya.
8
Amma kuma a wasu lokuta Karin hanyoyin kai-komo na ruwa yana sanya lissafin ya zama mai rikitarwa.
9
Na biyu: tasirin tattalin arziki. Kasuwar makamashi tana tasirantuwa sosai da haɗarin hanyoyi idan suka yi yawa.
10
Idan ana lissafa wasu hanyoyi safarar makamashi a matsayin masu hadari, tasirin yana shafar tashin farashi.
11
Na uku: ƙaruwar karfin ciniki. A kowane mataki na hulɗar ƙasa da ƙasa, samun ƙarin wasu hanyoyi yana nufin Karin karfin wasu da kuma raunin wasu.
12
Sai dai Wannan ba yana nufin illa ne ga dukkanin mu’amalar ba, a lokaci guda ma zai iya zama Karin tagomashi ne ga mu’amalar makamshi ta kasa da kasa.
13
A ƙarshe, wannan batu abu ne mai sauƙi: lokacin da yanayi ya samar da canji a cikin yanki, abu mafi dacewa shine dukkanin bangarori su yi aiki tare da hadin gwiwa domin cin gajiyar juna.