Rasha ta sha alwashin taimaka wa kasashen kawancen Sahel a fannin soji

Kasar ta sha alwashin ci gaba da taimakawa kasashen nan guda uku na kawancen sahel da suka hada da Mali, Burkina faso da kuma Nijar

Kasar ta sha alwashin ci gaba da taimakawa kasashen nan guda uku na kawancen sahel da suka hada da Mali, Burkina faso da kuma Nijar a fannin tsaro.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ne ya bayyana haka ranar Alhamis bayan ya gana da takwarorinsa na kasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar a birnin Moscow, yana mai cewa a shirye suke su taimaka domin bunkasa alaƙar soji da kasashen.

“Ina jaddada aniyar Moscow ta taimakawa domin samar da gamayyar rundunar soji ta yankin Sahel, tare da karfafa dakarun soji da sauran jami’an tsaro na wadannan kasashe uku ta hanyar ba su horo da makamai,” in ji Lavrov.

Wannan bayanin ya fito ne a yayin taron manema labarai da bangarorin suka gudanar a yayin wata ganawa da kasar ta Rasha a birnin Moscow.

Rasha ta tattauna da kasashen ne kan yadda za su bunkasa alakar soji, inda ta yi alkawarin bayar da horo da samar da makamai baya ga karfafa dangantaka tsakaninta da kasashen da ke yammacin Afirka da suka raba gari da kasar Faransa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments