Rasha Ta Jaddada Cewa: Kasashen Turai Sun Taka Doka Kan Batun Makamashin Nukiliyar Iran

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasashen Yamma sun taka dokokin kasa da kasa a batun Iran Mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasashen Yamma sun taka dokokin kasa da kasa a batun Iran

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar Rasha Sergei Ryabkov ya soki matakan ƙasashen Yamma, ciki har da harin soji da suka kai wa Iran da kuma ƙoƙarinsu na sake Sanya mata takunkumi, yana mai cewa, “A wannan yanayin, ƙasashen Yamma sun taka dokokin ƙasa da ƙasa.”

Jaridar Kommersant ta ruwaito cewa: Ryabkov ya yi waɗannan kalaman ne a lokacin wani shirin yanar gizo mai taken “Tarihi da Siyasar Yanzu na Manufofin Nukiliya na Rasha da Diflomasiyyar Jama’a a Bangaren Nukiliya,” wanda Cibiyar Makamashi da Tsaro ta shirya.

Yayi nuni da cewa: “Yanayin Iran, ƙasashen Yamma sun taka dokokin ƙasa da ƙasa da injin bulldozer, wanda ba za a yarda da shi ba kwata-kwata kuma babu adalci ciki, domin sun yi amfani da hanyoyi marasa kyau da ayyukan da ba su kan ƙa’ida.”

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Rasha ya jaddada cewa: Warware matsalar makamashin nukiliyar Iran siyasa ce da diflomasiyya, yana mai cewa, “Akwai hanyoyin magance wannan batu mai matuƙar muhimmanci a cikin umarnin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted