Rasha Na Tattaunawa Da Kasashen Afrika Kan Gina Tashoshin Nukiliya   

Shugaban Rasha ya nuna cewa wasu kasashen Afirka da dama sun nuna sha'awarsu ga tashoshin samar da wutar lantarki ta nukiliya.

Kamfanin Rosatom na kasar Rasha na tattaunawa da kasashen Uganda, Ghana, Habasha, da kuma Masar game da gina manyan tashoshin samar da wutar lantarki ta nukiliya.

Babban daraktan Kamfanin na Rosatom, Alexei Likhachev, ya ce Kasashe tara na Afirka sun kuma nuna sha’awarsu ga fasahar ta nukiliyar saman kan ruwa, a matsayin wani bangare na karfafa hadin gwiwa tsakanin Moscow da nahiyar.

Hadin gwiwar nukiliya yana daga cikin batutuwan da aka tattauna a taron koli na uku na Rasha da Afirka, wanda aka gudanar a wannan makon a Moscow, wanda wakilai daga wasu kasashen Afirka 50 suka halarta, ciki har da shugabannin kasashe da gwamnatoci.

An kaddamar da wannan dandalin a shekarar 2019, a wani bangare na dabarun Moscow na karfafa dangantakar siyasa da tattalin arziki da kasashen Afirka.

Bayan taron, shugaban Rasha Vladimir Putin ya nuna cewa wasu kasashen Afirka da dama sun nuna sha’awarsu ga tashoshin samar da wutar lantarki ta nukiliya, kananan fasahohin nukiliya, da kuma aikace-aikacensu a fannin likitanci da noma.

Alexei Likhachev ya kuma sanar da cewa ƙasashe tara na Afirka sun nuna “sha’awa mai mahimmanci” ga tashoshin samar da wutar lantarki da nukiliya da Rosatom ta gabatar.

A cewarsa, ana ci gaba da tattaunawa mai zurfi da Masar, Tanzania, Togo, da Namibia.

A halin yanzu nahiyar Afirka tana da tashar samar da wutar lantarki ta nukiliya guda daya kawai ta tashar Koeberg da ke Afirka ta Kudu, wadda aka gina ta amfani da fasahar Faransa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted