Rasha Na Karbar Taron Ministocin Harkokin Wajen Kasashen BRICS

Yau ake fara taron ministocin harkokin waje na kasashe mambobin kungiyar BRICS a kasar Rasha. Hadin gwiwar kasashe mambobin kungiyar da kuma manyan batutuwan shiyya-shiyya

Yau ake fara taron ministocin harkokin waje na kasashe mambobin kungiyar BRICS a kasar Rasha.

Hadin gwiwar kasashe mambobin kungiyar da kuma manyan batutuwan shiyya-shiyya da na kasa da kasa na cikin ajandar taron.

Ban da Iran, ministocin harkokin wajen kasashen BRICS 9 ne za su halarci taron, wanda za a yi a ranakun 10-11 ga watan Yuni.

Da yake magana da manema labarai ministan harkokin wajen Iran na rikon kwarya, Ali Bagheri Kani, ya ce wannan shi ne taro na farko da ministocin harkokin wajen kasashen BRICS zasu yi bayan Iran ta zama mamba a hukumance.

Mista Kani, ya kara da cewa : Kasancewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin wannan kungiya na nuni ne da matsayi da muhimmancin kasarsa a tsarin bangarori daban-daban na duniya.

Iran a hukumance ta zama mamba a kungiyar BRICS a farkon shekarar 2024, watanni biyar bayan amincewa da ita a matsayin cikakkiyar mamba a kungiyar tare da kasashen Argentina, Masar, Habasha, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Saudiyya.

A halin yanzu kasashen BRICS na da yawan jama’ar duniya kusan biliyan 3.5, tare da hadakar tattalin arzikin da ya kai sama da dala tiriliyan 28.5 ko kuma kusan kashi 28 na tattalin arzikin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments