Rasha : Iran Ta Mayar Da Martani Ne Bayan Dogon Lokaci Na Hakuri

Kasar Rasha ta ce wuce gona da irin Isra’ila ne ya tilasta wa Iran mayar da martani. Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya ne

Kasar Rasha ta ce wuce gona da irin Isra’ila ne ya tilasta wa Iran mayar da martani.

Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya ne Vasily Nebenzia ya bayyana hakan a taron gaggawa na kwamitin sulhu na ranar Laraba bayan Martanin Iran ga Isra’ila.

Wakilin na Rasha a MDD ya ce “Iran ta yi amfani da karfi ne bayan watanni biyu na kamun kai wanda ta nuna, amma duk da haka Isra’ila ta kara kaimi wajen kisan gilla.”

Mista Nebenzia, ya tabo batun halin da ake a gabs ata tsakiya a yayin taron gaggawa na kwamitin sulhu inda ya bayyana Allah wadai na kasarsa ga kisan Sayyid Hassan Nasrallah, shugaban kungiyar Hezbollah.

Ya kuma soki hare-haren da Isra’ila ke kai wa kasar Lebanon.

Jakadan na Rasha ya kara da cewa: “Wannan lamari barazana ne ga Lebanon da Gabas ta Tsakiya. »

“Na tabbata cewa Isra’ila ta san wannan sosai kuma da gangan ta yanke shawarar yin hakan,” in ji jami’in diflomasiyyar na Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments