Rahoton MDD : Isra’ila Ta Aikata Laifukan Yaki A Gaza

Wani sabon rahoto da MDD, ta fitar ya ce Isra’ila ta aikata laifukan yaki a lokacin yakin Gaza da aka faro tun daga ranar 7

Wani sabon rahoto da MDD, ta fitar ya ce Isra’ila ta aikata laifukan yaki a lokacin yakin Gaza da aka faro tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

Rahoton wanda wani kwamitin bincike na kasa da kasa na MDD, ya fitar ya gano cewa mahukuntan Isra’ila na da alhakin “Laifukan yaki kan bil’adama” da suka aikata a lokacin yakin Gaza.

Kwamitin ya gano cewar mahukuntan Isra’ila na da alhakin “laifukan yaki na yunwatarwa a matsayin makami da kisan jama’a da gangan da raba mutane da matsugunansu ta karfi da tsiya da fyade da cutarwa da muzantawa mai tsanani da tsare jama’a ba gaira babu dalili da keta mutuncin dan’adam.”

Haka zalika kwamitin ya gano cewa an aikata laifukan yaki da suka hada da “cin zarafin bil’adama da kashe rayuka da dama da zaluntar maza manya da yara kanana Falasdinawa da kisan kai da raba mutane da matsugunansu a Gaza.

An jikkata fararen hula da rushe gine-ginen fararen hula a Gaza, inji sabon rahoton.

Rahoton ya kara da cewa “Amfani da munanan makamai manya da ke iya yin barna a yankuna da gangan ya zama “harin ganganci kuma na kai tsaye a kan fararen hula.”

Haka kuma, kwamitin na MDD ya kaddara cewar gwamnatin Isra’ila tare da rundunar sojin kasar, “sun bayar da izini da bayar da dama da taimakawa ingiza” yakar falasdinawa a Yammacin gabar Kogin Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments