Rahoto: An yi tattaunawa mai tsawo tsakanin Syria da Isra’ila a Landan

Kafofin yada labaran Isra’ila sun rawaito cewa, an gudanar da wani dogon zaman tattaunawa a birnin London a yammacin jiya tsakanin ministan harkokin wajen Syria

Kafofin yada labaran Isra’ila sun rawaito cewa, an gudanar da wani dogon zaman tattaunawa a birnin London a yammacin jiya tsakanin ministan harkokin wajen Syria Asaad al-Sheibani da ministan kula da tsare-tsare na Isra’ila Ron Dermer, tare da halartar jakadan Amurka na musamman Tom Barak.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayyana cewa ganawar ta dauki tsawon sa’o’i biyar, inda bangaren Syria ya gabatar da martaninsa kan shawarar da Isra’ila ta gabatar na cimma yarjejeniyar tsaro, inda ta ce an samu ci gaba a tattaunawar.

A baya dai bangarorin biyu sun gana a zagaye na biyu da aka sanar, ban da kuma tarukan sirri da suka gudanar a lokuta daban-daban wand aba a sanar ba, da nufin kulla alaka ta siyasa da tsaro a tsakaninsu.

Shugaban rikon kwarya a kasar Syria, Ahmad al-Sharaa (Joulani) ya bayyana cewa, “Tattaunawar tsaro da Isra’ila za ta iya haifar da sakamako a cikin kwanaki masu zuwa,” duba da cewa “yarjejeniyar tsaro da Isra’ila ta zama wajibi kuma dole ne a mutunta sararin samaniyar Siriya da kuma yankunanta.”

Tun da farko majiyoyin Syria da Isra’ila sun bayyana cewa, wakilin Amurka Tom Barrack ne ya jagoranci taron, wanda ya gana da bangarorin biyu fiye da sau daya a wani yunkuri daidaita alaka tsakanin Syria da Isra’ila.

Jaridar Haaretz ta Isra’ila ta bayar da rahoton da ke cewa, daya daga cikin muhimman abubuwan da aka tattauna a taron tsakanin Dermer-Sheibani shi ne hana kungiyar Hizbullah ko sojojin Iran ko kuma duk wata kungiya da ake ganin tana adawa da Isra’ila kasancewa a kudancin Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments