Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce fiye da sojojin kasar 20,000 ne suka ji rauni tun farkon yakin da aka fara a Gaza a watan Oktoba 2023, inda fiye da rabinsu ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, ciki har da ciwon damuwa.
A cewar sashen bayar da shawarwari na ma’aikatar, kusan kashi 56 cikin 100 na wadanda suka ji rauni sun kamu da wasu matsalolin lafiyar kwakwalwa, wanda ke nuna irin tasirin matsalar kwakwalwa da wannan rikici ke haifarwa.
Ma’aikatar ta kara da cewa kusan kashi 45 cikin 100 na wadanda suka ji rauni suna fama da raunuka a jiki, yayin da kashi 20 cikin 100 na sojojin ke fama da matsalolin kwakwalwa da na jiki a lokaci guda.