Qatar Na Ci Gaba Da Kokarin Diflomasiya Don Cimma Yarjejeniya

kasar qatar ta na ci gaba da kokari diflomasiya na ganin an cimma yarjejeniya tsakanin iran da Amurka

Fira ministan kasar Qatar da ministan harkokin wajen kasar mohammad bin abudrrahman bin jassim ali thani sun jadda game da kokarin da kasarsa ke yi na diflomasiya na ganin an cimma wata yarjejeniya tsakanin kasar Amurka da kuma kasar iran, yace yarjejeniyar za ta taimaka wajen samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin

Babban jami’ain na kasar Qatar yayi wannan bayanin ne a tattaunawa da suka yi ta wayar tarho da ministan harkokin wajen iran Abbas araqchi da kuma wani kwararre dan kasar jodan ayman safadi kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta wallafa

Jami’an kasashen biyu sun tattauna ne kan ci gaban da aka samu a yankin, da kuma dangantakar dake tsakanin Doha da amman ,kuma tattaunawar ta karkata ne kan tsarin diflomasiya da aka bullo da shi da kuma yin aiki tare domin rage kaifin rikici da kuma karfafa zaman lafiya da tsaron yanki

Daga karshe al thani ya jaddada goyon bayan kasar Qatar kan duk wani kokarin diflomasiya da zai bude hanya wajen ganin an kulla yarjejeniya tsakanin iran da Amurka da zimma samar da dawamamman zaman lafiya da tsaro a yankin

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted