Hizbullah: Babu wani matsayi da aka rasa wanda ba a cike gurbinsa ba

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya tabbatar da cewa, duk da asarori na manyan mutane da kungiyar Hizbullah ta yi, amma komai

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya tabbatar da cewa, duk da asarori na manyan mutane da kungiyar Hizbullah ta yi, amma komai nata yana cikin tsari .

A cikin wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin na tunawa da zagayowar ranar da kungiyar Hizbullah ta fara gudanar da ayyukan nuna goyon baya ga al’ummar Gaza bayan fara kaddamar da hare-haren kiyashi na Isra’ila a kansu wato ranar 8 ga Oktoba, 2023, Sheikh Qassem ya sake tabbatar da cewa,  “Ba mu da wani mukami da ba kowa a kansa a cikin Hezbollah; dukkan mukamai da aka rasa akwai masu tafiyar da su kamar yadda yake a cikin tsarin kungiyar.

Ya bayyana cewa Hizbullah za ta zabi Sakatare-Janar kamar yadda ka’idar jam’iyyar ta tanada, wanda za a sanar a lokacin da ya dace.

Sheikh Qassem ya tabbatar da cewa, kwarewar da shugabannin bangarorin Hizbullah da aka rasa suke da ita, a bayyane takea  wajen mataimakansu, da kuma wadanda suke maye gurbinsu.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Lebanon tana ba su hadin kai, kamar yadda komai yana tafiya bisa tsari a fagen daga.

Ya ci gaba da cewa: “Wannan yakin ba zai taba yin tasiri a kan manufofinmu da suka shafi makiya ba, domin kuwa abin da mayakan Hizbullah suke a fagen daga ya tabbatar da azamarsu wajen ci gaba da bin tafarkin Sayyid Hassan Nasrallah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments