Qalibof: Asarorin HKI A Yakin Kwanaki 12 Yafi Abinda Ta Bayyana

shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibof ya bayyana cewa asarorin da HKI ta yi a yakin kwanaki 12 da JMI suna da yawa.

shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibof ya bayyana cewa asarorin da HKI ta yi a yakin kwanaki 12 da JMI suna da yawa. Kuma babu shakka ya fi abinda ta bayyana.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban majalisar dokokin kasar ta Iran yana fadar haka a lokacinda yake hira da wata tashar talabijin a nan Tehran . Ya kuma kara da cewa. Maganar cewa uahudawa 3500 kawai suka ji rauni a yakim gaba daya karya ce.

Qalibof ya ce yana da tabbacin cewa yahudawa akalla 500 suna halaka sanadiyyar hare-haren da sojojin Iran suka kai a kan HKI a yankin kwamaki 12. .

Ya ce sojojin yahudawan sun saba boye yawan mutanen da suka halaka a yake-yaken da take fafatawa da masu gwagwarmaya a yankin. suna kuma hana yada hutunan bidyo na asarorin da suka yi a yaki. masili daga cikin wasu da dama shi ne yadda suka hada yar rahoton tashar talabijin ta Aljazeera daukar hotuna a yakin saboda basa son muatane su san gaskiya. su kuma ga irin yawan asarorin da suka yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted